Nazarin Al'adun Zamantakewar Hausawa da na Al'ummomin Garin Gombi Jihar Adamawa
Keywords:
al'adu, al'ummomi, Gombi, Hausawa, zamantakewaAbstract
Wannan takardar mai taken ‟Nazarin Al'adun Zamantakewar Hausawa da na Al'ummomin garin Gombi, Jihar Adamawa”, ta yi tsokaci ne kan irin gudummawar da kyakkaywar zamantakewar da Hausawa suka bayar wadda ta haifar ga ci gaban al'ummomin a yau. Takardar ta yi waiwayen taƙaitaccen tarihin Hausawa da zuwansu garin tare da ɗan abin da ba a rasa ba na daga tarihin garin Gombi. Sannan Manufar wannan bincike ita ce bayyanar da wanzuwar Hausawa, da nazartar zamantakewarsu da sauran al'ummomin garin tare cike giɓin da aka bari a fannin ilmi. Haka nan an ɗora wannan aiki ne kan ra’in sauyesauyen al’adu (al’umma) wanda Charlse
Darwin ya ƙirƙira a shekarar 1958. Wannan ra’i yana bayani ne game da sauyesauye da suke faruwa ga al’umma ko al’adunsu daga wani matsayi zuwa wani, kamar yadda kyakkyawar zamantakewar Hausawa ya samar da ci gaban al'ummomin garin Gombi daga matsayinsu na da, ya zuwa matsayin da suke a yanzu. Hanyoyin tattara bayanai kuwa, sun haɗa da yin hira da masana tare da sanya idanu game da rayuwar al'ummomin Gombi. Daga ƙarshe binciken ya gano irin tasirin da kyakkyawar zamantakewar Hausawa ya haifar ga ci gaban al'ummomin a ɓangarori kamar: harshe da tufafi (sutura) da sarauta da bukukuwa da abinci da makamantansu.