In’ina a Hausa: Nazarin Furuci da Gava da Kalma da kuma Ma’ana
Abstract
A wannan takarda an yi nazari a kan in’ina, wanda ya shafi ma’anarta da taqaitaccen tarihinta da ire-irenta da halaye da siffofin da masu yin ta ke shiga a lokacin magana da alamomi zuwanta da ma vangarorin furuci da take shafa. An gudanar da wannan nazari ne
ta hanyar tattaunawa da masana harshe da lokitoci da kuma masu matsalar in’ina, tare da nazarin wasu littattafai da takardu waxanda suka shafi harshe musamman harshen Hausa. Sannan an duba yanayin da masu yin in’ina kan kasance tare da bayyana wasu sassan
furuci da take shafa. Nazari ne da ya shafi masu in’ina musamman Hausawa, domin ganin yadda take da yadda ake yin ta da yadda ta ke shafar furucin magana da fahimtar ma’ana.
Downloads
Published
2024-12-05