Bara a Tunanin Bahaushe: Nazari daga Tsangaya
Keywords:
Tunani, Bahaushe, TsangayaAbstract
Wannana muƙala ta yi amfani da ra’in zuwa-da-kai ya-fi -saƙo wato ethnographic theory wajen binciko tunanin Bahaushe dangane da bara. Binciken ya gano a farkon lamari almajiranci ba shi da alaƙa da bara. Bara daban almajiranci ma daban. Daga baya ne saboda wasu dalilai bara ta kunno kai a harkan almajiranci. Haka kuma binciken ya gano kallon da Bahaushe yake yi wa bara ya sha bamban da yadda sauran jama’a da ba su da alaƙa da almajiranci suke ganin ita bara domin shi Bahaushe ba ya ganin munin bara ta almajirai ta kai a hana almajiranci. Duk kuwa da ya yarda in da za a samar da wata hanya da ba sai almajirai sun yi bara ba, da ya fi. Haka kuma
binciken ya gano dadewar bara a harkar almajiranci ta sa Bahaushe na ganin akwai albarka da kuma amfani da ake samu dangane da barar almajirai. Daga ciki akwai hada lakanin karatu da tuwan barar da almajiri ya samu a bararsa ta farko idan ya je almajiranci. In an yi wannan lakanin almajiri yakan fahimci karatu da wuri. Daga karshe binciken ya ba da shawarar hukumomi da kungiyoyi masu zaman kansu su rika kokarin fahimtar tunanin allarammomi da almajiransu kafin daukan duk wani mataki ko aiwatar da wani shiri da ya shafi almajiranci. Hakan zai taimaka a fahimci hanyar da za a taimaka wa almajiranci tare da hadin kan wadanda abin ya shafa.