Adabin Kasuwar Kano Jiya da Yau

Authors

  • Sumayyat Ibrahim Gambo
  • Sunusi Gambo Bello
  • Nura Musa Jamilu

Keywords:

Adabi, madubin rayuwa, kasuwar Kano, lamari

Abstract

Adabi a matsayinsa na hoto ko madubin rayuwa wanda yake sassauyawa daga lokaci zuwa lokaci. Irin wannan sauyin a wasu lokutan kan haifar da tsirar wani lamari daga cikin adabin ko kuma sauyin fasali a sakamakon haɗuwar al’umma da wasu baƙi. Wannan takarda ta yi ƙoƙarin bin diddigin yadda adabin kasuwar Kano ya faro da kuma halin da yake ciki a yanzu. An yi nazarin litattafan magabata da suka shafi wannan nazari, tare da yin amfani da hanyar hira da asalin marubuta litattafan ƙagaggun labaran da ake kira da adabin kasuwar Kano, don ganin an sami madogara dangane da bayanan da aka yi cikin wannan takarda. A taƙaice, nazarin ya gano cewa; da farko lamarin ya sami karɓuwa ta fuskar marubuta, inda aka sami marubuta da dama da kuma litattafansu. Haka nan, a ɓangaren masu karanta litattafan, su ma ba a bar su a baya ba, inda har gidajen ba da haya ake da su ga waɗanda ba su da ƙarfin saya. Sa’annan, litattafan sun taimaka wurin gyara mu’amala da kuma zamantakewa ta fuskoki daban-daban ga masu karanta su. Amma a yanzu, al’amarin ya taɓarɓare, inda masu karanta litattafan suka yi ƙaranci sosai, hakan ya sanya marubuta da dama barin harkar. Sannan ɗan waɗanda suka rage, sun fi mayar da hankali kan sayar da litattafan a yanar gizo, maimakon buga su kamar yadda aka saba.

Published

2024-02-16