Sharhi kan Jigon Bijirewa a wasu Waƙoƙin Siyasa na wasu Jihohin Arewa Maso Gabas na Najeriya

Authors

  • Ali Ahmadi Alƙali
  • Shehu Halilu

Keywords:

Waƙoƙin Siyasar, Arewa Maso Gabas na Najeriya, jigon bijirewa, jawo hankalin al`umma kan manufofin gwamnati

Abstract

Wannan aiki mai taken “Nazarin Jigon Bijirewa a wasu Waƙoƙin Siyasar Arewa Maso Gabas na Najeriya “. Waƙa rubutacciya ko ta Baka hanya ce ta isar da saƙonni ga al`umma, ta hanyar ilmantarwa da faɗakarwa da kuma nishaɗantar da jama`a tsawon lokaci. Waƙoƙin Hausa suna tallafawa wajen yayata harkokin siyasa. Misali a lokacin yankar katin zaɓe da lokacin kamfen da jefa Ƙuri`a. Mafi yawancin ayyuka da manazarta suka yi a kan waƙoƙi sun ta`allaƙa ne a kan zubi da tsari ko salon sarrafa harshe da ma wasu jigogi na musamman. Bincike kan jigon bijirewa bai yi yawa ba a wannan zamani, sai dai a baya akwai waɗanda aka yi a kan siyasar jamhuriya ta ɗaya har zuwa ta huɗu. An ɗora aikin a kan ra`in Markisanci da ke bayani a kan yadda ake amfani da fasaha ta Adabi don jawo hankalin al`umma kan manufofin gwamnati, ko su runguma ko kuma su kauce don illar da manufofin ke iya jawo masu. Akwai waƙoƙin masu jigon bijirewa da ke bayanin bijirewar da ɗan siyasa ya yi wa jam`iyyar da yake ciki ko zuwa wata jam`iyyar ko kuma yana ciki amma yana nuna rashin gamsuwar sa a kan wasu manufofin ko halayen da ake nunawa a jam`iyyar wani lokacin hujjojin na laifin da ya shafi karan kansa ne wani lokacin kuma na a`lumma. A wannan aikin an yi amfani ne da waƙoƙi guda uku, waƙar “Ta Ɓare Ba da Mu Ba” ta Dauda Kahutu Rarara jihar Adamawa, sai wakar “Za Ku Ga Hujinsa” Ta Yusuf Dauda Nabargu jihar Bauchi sai kuma “Mun Ƙaura Zuwa NNPP” wacce Haruna Umar ya yi a jihar Taraba. A cikin wannan binciken an gano cewa lallai akwai waƙoƙin masu jigon bijirewa a harkokin siyasa da mawaƙa kan yi kuma waɗannan waƙoƙin suna ɗauke da bayanan hujjojin bijirewar da ma jam`iyyar da aka nufa bayan an baro wacce ake ciki, tare da nuna irin moriyar da ake ganin an zowa sabuwar da ita da baya ga nuna irin rashin da wace aka baro ta yi. Akwai buƙatar faɗaɗa wannan aikin ya zuwa wasu sauran jihohi ba arewa maso gabas ba kawai har ma da sauran jihohin ƙasa baki ɗaya don ƙara tabbatar da wanzuwar wannan jigon daga wajen masu bincike, wannan shi ne shawarar da na gabatar.

Published

2024-02-16