Waƙoƙin Yara a ƙarni na 21: Fassara da Nazarin Zaɓaɓɓun Waƙoƙi na Turanci

Authors

  • Usman Musa Nakaka
  • Muhammad Garba
  • Shehu Umar Kafi

Keywords:

waƙoƙin yara a ƙarni na 21, waƙoƙi daga Turanci, fassararrun waƙoƙin, dabarun rera waƙoƙin

Abstract

Binciken ya nazarci waƙoƙin yara a ƙarni na 21, ƙarƙashin fassara da nazarin zaɓaɓɓun waƙoƙi daga Turanci. Sannan aka aiwatar da nazarin bisa Abba da Zulyadaini (2000) da kuma Ɗangambo (2007), haɗe da kwaikwayon Dumfawa 2011. A ƙarshen maƙalar akwai nasarori, waɗanda suka ƙunshi: fassara waƙoƙi daga Turanci zuwa harshen Hausa. Waƙoƙin su ne: (1) Two Little Dickie Birds (2) Hokey Cokey (3) My Mother (4) Head, Shoulders, Knees and Toes (5) Johny Johny Yes Papa (6) Do Your Ears Hang Low (7) Twinkle Twinkle Little Star (8) Thirty Days Hath September (9) Roses are Red (10) Early to Bed Early to Rise. Sai aka nuna yadda fassararrun waƙoƙin, suka koma waƙoƙin baka cikin Hausa, tare da kawo nazari mai jagoranta, game da salon jigon ilimantarwa, da kuma dabarun rera waƙoƙin koyarwa, haɗe da tasirin ƙirga adadin kalmomi, musamman cikin waƙoƙi daga harsuna; Turanci da Hausa.

Published

2024-02-16