Ajami Gagara Mai Shi: Dabarun Koyar da Ajamin Hausa

Authors

  • Muhammad Garba
  • Usman Isa Nakaka
  • Shehu Umar Kafi

Keywords:

karatu da kuma, rubutun ajami, Kaxan Zuwa Yalwa

Abstract

Wannan bincike ya karkata ne kan koyo da koyar da karatu da kuma rubutun ajami. Koyarwa na nufin ilimantar da mai koyo don a sa masa wasu canje-canje cikin rayuwa; Ajami hanya ce ta rubutun Hausa cikin harufan Larabci. Ɗaliban manyan makarantu suna fuskantar barazana da hangen tsauri, wajen ɗaukar kwas mai koyar da Ajami. Kuma qarancin daidaitattun hanyoyin koyar da xaliban, ya taimaka bisa qalubalen. Nazarin ya gudana bisa kwaikwayon Yahaya 1988, tare da zavo hanyar da ake kira: “Kaxan Zuwa Yalwa” watau, Inductive Method. Nazarin ya xauki aikin daki-daki; bisa yadda za a koyar da karatu, tare da rubuta baqaqe da wasula da ginin gava da kalma, har ya zuwa ginin jimla, qarqashin dokokin daidaitacciyar Hausa.

Published

2024-02-16