Nazarin Darasu a Tsangaya

Authors

  • Yahuza Usman Musa
  • Ginsau Abdulƙadir

Abstract

Ilimin Alqur’ani muhimmin abu ne a rayuwar Musulmi. A arewacin Nigeriya musamman a da can neman ilimin Alqur’ani ana yin sa ne kawai ta hanyar tura yara da aka fi sani da almajirai tsangaya da kuma makarantun allo. A waxannan wurare ne yaro zai fara samun karatun Alqur’ani tun daga babbaqu da farfaru da biye da kuma hadda. Almajiri ba ya zuwa mataki na gaba sai an yi masa darasu ya yi ta biyawa ya kuma iya. Wannan darasu da ake yi wa almajirai shi ne wannan takarda ta binciko domin ganin mene ne shi. Yaya ake yin sa da rabe-rabensa da laddubansa da muhallinsa da kuma masu yinsa. An yi amfani da ra’in Gani-Ya-Kori-Ji wato Ethnographic Theory. Ra’i ne da yake ƙarfafa cewa hanya mafi inganci na nazarin al’ada ita ce mai nazari ya yi bulaguro ya shiga cikin mutanen da zai nazarta ya yi mu’amala da su ya tattauna da su ya kuma gane wa idonsa yadda suke aiwatar da wannan al’adar. Ta wannan hanyar ce wannan bincike ya gano darasu wanda hanyace da malami yake biya wa almajiri karatunsa da kuma yi masa gyare-gyare yana da rabe-rabe da suka haxa da darasun sara da darasun doro da darasun zube da darasun awaki. Haka kuma masu darasu sun haxa da babban Malam da buna da gardawa.Baya ga nan binciken ya gano darasu yana da muhallin yin sa da kuma laddubansa.

Published

2025-05-09