Adashi Jiya da Yau: Nazari a kan Sana`ar Adashi a Birnin Kano.
Keywords:
Al‘ada da, Adashi, Sana’aAbstract
Wannan takrda ta yi bayani neakan yadda ake gudanar da sana`ar Adashi tsakanin al`ummar Hausawa, ytare da nuna wannan sana`a an jima ana yinta. Wannan takarda ta yi tsokaci ne akan wannan sana`a, musamman ta fuskar taimakon juna da nuna haxinnkai tsakanin jama`a. Wannan takarda ta yi amfani da hanyoyin tattaunawa da mutane da suke da ruwa da tsaki a kan wannan sana`a. Haka muka wannn takarda an xora ta ne a kan ra`in adana al`ada (cultural sustaibability theory). A qarshe wannan takarda ta fito da sakamakon bincike kamar haka, wannan sana`a hanya ce ta taimakon juna tsakanin al`umma da kuma dogaro da kai. Sannan wannan bincike ya gano cewa wannan sana`a tana taimakawa wajen havakar tattalin arzikin al`umma amusamman a tsanin masu ta`ammali da ita. Haka kuma , wannan sana`a hanya ce ta adana tsohuwar al`ada da al`umma suka amfana da ita tun da daxewa.
