Nazarin Littafin Zuciya da Qwanji: Duba kan Jigo da Salo da Taurari

Authors

  • Yunusa Ibrahim Adamu
  • Ruqayya Ahmad Kari

Abstract

Manufar wannan takarda ita ce a fayyace Nazarin littafin Zuciya da Qwanji, wanda mawallafiya Maimuna Idris Beli ta wallafa. An yi amfani da Mazhabar Xangambo, 1990, wajen xora wannan bincike. Haka kuma an yi amfani da sharhantaccen bincike bi-bayani
(Desarviptive qualitative method) wajen gudanar da wannan bincike. Haka kuma an yi duba na tsanaki a cikin littafin ta hanyar yin karatun nazari domin fito da jigo da salon wannan littafin. Haka kuma binciken ya gano yadda marubuciyar ta yi amfani da babban jigon littafin shi ne ‘gargaxi’ wannan gargaxi an yi shi ne game da masu yin auren kisan wuta, inda mawallafiyar ta yi amfani da jigo tahaqiqi wajen fito da jigon littafin. Sannan akwai wasu daga cikin qananan jigogi da wannan bincike ya gano da suka haxa da soyayya da kishi da sadaukarwa da kyautatawa da sauransu. Haka kuma binciken ya gano cewa mawallafiyar ta yi amfani da miqaqqen salo wanda ya haxa da baxoki da xarsau da hoto cikin bayani da amfani da hotuna da zane-zane da aron kalmomi. Haka kuma binciken ya gano yadda mawallafiyar ta yi amfani da adon harshe a cikin labarin da suka haxa da Karin magana da baqar magana da sauransu. Ta fuskar shawarwari, zai yi kyau manazarta adabin Hausa su mayar da hankali wajen inganta wannan fanni na qagaggun labarai, saboda samar da yanayi mai kyau wajen samar da cigaban adabin ta fuskar koyo da koyarwa musamman a makarantun Sakandare da na gaba da Sakandare har zuwa jami’a.

Published

2025-05-09